Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya

Ana zanga-zanga a Bangui

Rahotanni daga Jamhuriyar Afrika ta tsakiya na cewa daruruwan mutane sun fito saman titi suna zanga-zanga a birnin Bangui domin nuna adawa da matakin da kwamitin sulhunta bangarorin rikicin kasar ya daukagame da makomar kasar bayan shafe tsawon mako ana tattaunawa.

Taron sasanta rikicin Afrika ta tsakiya da Catherine Samba-Panza ke jagoranta a Bangui.
Taron sasanta rikicin Afrika ta tsakiya da Catherine Samba-Panza ke jagoranta a Bangui. AFP PHOTO / PACOME PABANDJI
Talla

Masu zanga-zangar sun mamaye birnin Bangui tare da yin kira ga shugabar rikon kwaryar kasar ta yi murabus bayan kwamitin ya bayar da shawarar tsawaita wa’adin gwamnatin tare da dage zaben kasar zuwa watan Agusta.

Wakilai kusan 600 ne suka halarci taron sasanta rikicin Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya a Bangui, amma a daidai lokacin da ake gudanar da bikin rufe taron, wasu mutane dauke da makamai suka rika yin harbi a wajen ginin Majalisar dokoki inda aka gudanar da taron.

Taron dai bai bayyana ranakun da za a gudanar da zabuka a kasar ba, amma Shugabar rikon kwarya Catherine Samba-Panza ta sha alwashin cewa za a yi zaben kafin karshen 2015.

Masu zanga-zangar dai sun kona tayu tare da toshe manyan hanyoyin birnin Bangui da ke zuwa tashar jirghin sama.

Amma rahotanni daga Afrika ta tsakiya na cewa ‘Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar.

A watan Maris din 2013 ne dai rikici ya barke a Afrika ta tsakiya bayan magoya bayan shugaban kungiyar Seleka yawancinsu Musulmi Michel Djotodia sun hambarar da gwamnatin Francios Bozize, lamarin da ya sa rikicin kasar ya rikide zuwa na babbancin addini da kabilanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.