Afrika ta tsakiya
‘Yan tawaye za su saki yara da aka ba Makamai a CAR
Majalisar Dinkin Duniya tace ‘Yan Tawayen kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun amince su mika yara kanana da suka sanya cikin aikin soji da kuma wadanda ake lalata da su. Kungiyar UNICEF tace kungiyoyi 8 suka sanya hannu kan yarjejeniyar kuma ana saran mika yara tsakanin 6,000 zuwa 10,000 da ke karkashinsu.
Wallafawa ranar:
Talla
An dai kwashe mako guda ana tattaunawa kafin ‘yan tawayen su amince da shirin a matsayin matakin farko na sasanta rikicin kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu