MDD ta gargadi Afrika ta tsakiya akan ‘Yan gudun hijira
Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi hukumomin kasar Jamhuriyar Afirka ta tsakiya kan daukar duk wani mataki na hana ‘yan gudun hijirar kasar shiga zaben da za a yi a watan Oktoba mai zuwa.
Wallafawa ranar:
Mai Magana da yawun hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Leon Dobbs ya ce ya zuwa yanzu ‘yan gudun hijira kusan 200,000 Musulmi ke zama a sansanin da ake kula da su, inda ya ke cewa hana su zabe zai yi matukar illa ga sahihancin zaben.
Majalisar tace akalla ‘yan kasar kusan 500,000 suka gudu daga kasar don tsira da rayukan su.
Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ta fada cikin rikici ne tsakanin Mayakan Seleka musulmi da kuma anti balaka kirista a lokacin da Michel Djotodia na Seleka ya jagoranci hambarar da gwamnarin Francios Bozize.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu