Isa ga babban shafi
Afrika taTsakiya

Tsohon Firaministan Bozize ke kan gaba a zaben Afrika ta tsakiya

Tsohon Firaministan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin Archange Touadera na kan gaba da yawan kuri’u a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Laraba 31 ga watan Disemba.

Tsohon Firaministan Afrika ta tsakiya Faustin-Archange Touadéra
Tsohon Firaministan Afrika ta tsakiya Faustin-Archange Touadéra (Photo : AFP)
Talla

Rahotanni sun ce Tsohon Firamnistan ya samu kashi 23 na kuri’un da aka kidaya kashi daya bisa hudu.

Touadera mai shekaru 58 ya taba yi wa shugaba Francois Bozize Firaminista tsakanin shekarar 2008 zuwa 2013, kuma kafin zaben ba ya cikin wadanda ake ganin zasu iya samun nasara.

‘Yan takara 30 ne suka shiga zaben na Jamhuriyyar Afrika Afrika ta tsakiya mai fama da rikici.

Tsohon Firaministan da ya tsaya a matsayin dan takarar indifenda ya samu kuri’u sama da 120,000, yayin da Anicet Georges Dologuele, wanda shi ma ya taba rike mukamin Firaminista yake bi ma shi da kuri’u 68,500.

A ranar 31 ga watan Janairu ne za a je zagaye na biyu a zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.