Isa ga babban shafi
Afrika taTsakiya

Ana gudanar da zabe a Afrika ta Tsakiya

Yau al’ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ke gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu.

Al-ummar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu
Al-ummar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu MARCO LONGARI / AFP
Talla

Zaben na yau zai nuna irin ci gaban da aka samu na ganin kasar ta koma turbar demokiradiya bayan juyin mulkin shekarar 2013 da ya jefa kasar cikin rikicin addini da kabilanci.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi kiran samun karbabben zaben da duniya za ta amince da shi a Janhuriyar Afirka ta Tsakiya mai fama da tashin hankali.

Dakarun samar da zaman lafiya 11,000 za su taimaka wa al’ummar kasar don ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.