Isa ga babban shafi
Ghana

Shugaban Ghana zai gina asibitoci 88 cikin shekara 1

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya sha alwashin gina sabbin asibitoci masu inganci guda 88 a sassan kasar domin shawo kan karancin su, bayan matsalar da aka gani sakamakon annobar coronavirus.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo. John MacDougall/Pool/AFP via Getty Images
Talla

Shugaban ya bayyana haka ne a jawabin da ya yiwa al’ummar kasar karo na 8 kan halin da ake cikin dangane da kokarin gwamnati na yakar annobar coronavirus, da kuma matakan da take dauka wajen aiwatar da dabarun dakile cutar.

00:55

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo kan gina asibitoci 88 a shekara 1

Ranar litinin shugaban na Ghana Nana Akufo-Addo yayi shelar tsawaita dokar hana tarurrukan jama’a da karin makwanni biyu, a cigaba da kokarin dakile cutar coronavirus.

Ranar 15 ga watan maris gwamnatin Ghana ta soma kafa dokar haramta tarurrukan jama’a, bayan tabbatar da rahoton kamuwar mutane 2 da cutar coronavirus, karo na farko a kasar.

Zuwa ranar lahadi 26 ga watan Afrilu jami’an lafiya a Ghana ta yi nasarar yiwa ‘yan kasar akalla dubu 100 da 622 gwajin cutar coronavirus, daga ciki kuma an tabbatar da kamuwar dubu 1 da 550, ciki harda mutane 11 da suka mutu, yayinda wasu 155 suka warke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.