Isa ga babban shafi
Ghana

Ghana ta janye dokar hana zirga-zirga

Shugaban Ghana Nana Akufo Addo ya janye dokar takaita zirga-zirga ta tsawon mako uku wadda aka kafa a wasu yankunan kasar don hana yaduwar cutar coronavirus, yana mai cewa, dokar ta jefa talakawa cikin mawuyacin hali.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo premiumtimesng
Talla

A wani jawabi da ya yi wa al’ummar kasar ta kafar talabijin, shugaban ya ce, sun dauki matakin janye dokar ce saboda ci gaban da aka samu wajen takaita yaduwar coronavirus da kuma tasirin dokar kan talakawa da masu rauni.

Kodayake har yanzu akwai haramcin taruwar jama’a, sannan kuma iyakokin kasar za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Shugaban ya bukaci al’ummar kasar da su rika sanya kyallayen rufe baki da hanci don kare kansu daga kamuwa da annobar.

Tun a franar 31 ga watan Maris da ya gabata, manyan biranen kasar da suka hada da Accra da Ashanti suka kasance a rufe bayan an samu mutane 137 da suka harbu da COVID-19.

Yanzu haka a jumulce, mutane dubu 1 da 42 ne suka harbu da cutar a kasar, yayin da 9 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.