Dokar hana fita ta fara aiki a lardunan Accra da Kumasi na Ghana
Gwamnatin kasar Ghana ta haramta zirga-zirga a yankuna biyu mafi girma a kasar daga wannan litinin, domin dakile yaduwar cutar COVID-19 da ke ci gaba da halllaka jama’a a kasashen duniya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban kasar Nana Akufo-Addo ya ce daukar matakin ya biyo bayan samun mutane 137 da suka kamu da cutar, yayin da tuni 4 suka rasa rayukansu.
Akufo-Addo ya bayyana yankunan da suka hada da Accra da kuma Kumasi, to sai dai ya ce matakin bai hana mutane fita domin sayen abinci da ruwan sha da magunguna ba, ko kuma amfani da ban dakin jama’a.
Shugaban ya ce dokar ta makwanni biyu ta haramta zirga zirgar jama’a daga gari zuwa gari a mota da jiragen sama, sai dai wadanda jami’an kula da lafiya ke aiki da su kawai.
Tuni Ghana ta bi sahun kasashen duniya wajen rufe makarantu da dakatar da ayyukan gwamnati da kuma hana taron jama’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu