Isa ga babban shafi
Ghana

Mutanen Ghana za su sha ruwan famfo kyauta

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya bayyana cewar al’ummar kasar za su kwashe watanni 3 suna shan ruwan famfo ba tare da biyan sisin kwabo ba, a wani yunkurin saukaka musu radadin zaman gida saboda takaita yaduwar cutar coronavirus.

Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo REUTERS/Luc Gnago
Talla

Shugaban ya kuma bai wa kamfanonin samar da ruwan da na samar da wutar lantarki da su tabbatar sun wadata jama’a a wannan lokaci.

A yayin yi wa al’ummar kasar jawabi, shugaban ya kuma sanar da tsawaita dokar rufe iyakoki na karin makwanni biyu saboda rahotannin masana kiwon lafiya da ke nuna cewar akasarin wadanda aka samu da cutar a Ghana sun fito ne daga kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.