Isa ga babban shafi

Likitocin Ghana 13 sun kamu da cutar coronavirus

Kungiyar likitocin kasar Ghana tace akalla manbobinta 13 sun kamu da cutar coronavirus.

Wata jami'ar kiwon lafiya rike da na'urar gwajin kwayoyin cuta.
Wata jami'ar kiwon lafiya rike da na'urar gwajin kwayoyin cuta. Reuters+
Talla

Shugaban reshen kungiyar likitocin ta GMA na yankin Ashanti, Paa Baidoo ne ya sanar da kamuwar likitocin a yau talata.

Dakta Baidoo ya dora alhakin aukuwar lamarin kan rashin isassun kyayyakin baiwa likitoci kariya daga kamuwa da cutar ta COVID-19.

Zuwa ranar talatar nan 28 ga watan Afrilu, yankin Ashanti ke kan gaba a kasar Ghana wajen yawan wadanda da suka kamu da cutar coronavirus, da adadin mutane 69.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.