Isa ga babban shafi
Afrika

Al'ummar Namibia na shirin kada kuri'a a babban zaben kasar

Al’ummar Namibia na shirin kada kuri’a a babban zaben kasar da ke tafe ranar Laraba mai zuwa, zaben da ke zuwa dai dai lokacin da jama’a ke kukan tsanantar talauci da tabarbarewar tattalin arziki.

Shugaban kasar Namibia Hage Geingob
Shugaban kasar Namibia Hage Geingob Reuters
Talla

Namibia wadda ke yankin kudu maso yammacin Afrika na cikin jerin kasashen nahiyar da ke da tarin albarkatun karkashin kasa amma kuma ta ke fuskantar mulkin kama karya daga hannun jam’yya guda tun bayan samun ‘yanci a shekarar 1990.

Kuri’ar jin ra’ayin jama’a dai ta nuna ba lallai shugaba Hage Geingob mai shekaru 78 ya kai labari a zaben ba, wanda yak e neman karin wa’adin mulkin kasar, inda a yanzu haka wasu fusatattun matasa ke ci gaba bore don nuna adawa da matakinsa na sake tsayawa takara.

Akwai dai kwakkaran hasashe da ke nuna cewa Panduleni Itula tsohon jami’in lafiya mai shekaru 62 ya iya kai labari a zaben la’akari da yadda yake da magoya baya hatta daga jam’iyya mai mulki ta SWAPO.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.