Isa ga babban shafi
Sudan

Kotu ta tsaida ranar yanke hukunci kan al-Bashir

Kotu a Sudan ta bayyana 14 ga watan Disamba mai zuwa a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan tsohon shugaban kasar Oumar al-Bashir, dake fuskantar tuhume-tuhume kan aikata laifukan cin hanci da rasahawa da halasta kudaden haram.

Tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir yayin gurfana a gaban kotu.
Tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir yayin gurfana a gaban kotu. REUTERS/Mohamed Nureldin Abdallah
Talla

Kafin soma zaman shari’ar a watan Agusta, jami’an tsaro sun gano euro miliyan 6 da dubu 9, dala dubu 351, da kuma fam din Sudan miliyan 5 da dubu 700, duka a gidan tsohon shugaban kasar, kudaden da yace ragowa ne na jimillar dalar Amurka miliyan 25 da yarima Muhd bin Salman na Saudiya ya bashi.

A watan Afrilun da ya gabata, sojoji suka kifar da shugabancin al-Bashir bayan da dubban ‘yan kasar suka shafe watanni, suna zanga-zangar adawa da gwamnatinsa.

A dai dai lokacin da al-Bashir ke fuskantar shari’a a Khartoum, kungiyoyin kare hakkin dan adam da dama na kiraye-kirayen hukunta tsohon shugaban na Sudan bisa aikata laifukan yaki a yankin Darfur., ta hanyar mika shi ga kotun duniya ICC.

Kotun ta ICC na zargin tsohon shugaban na Sudan da hannu wajen aikata kisan kare dangi, laifukan yaki, da cin zarafin dan adam yankin Darfur dake yammacin kasar Sudan, inda a 2003, yakin basasa ya barke tsakanin mazauna yankin bakar fata da da labarawa farar fata.

Majalisar dinkin duniya tace kimanin mutane dubu 300,000 suka halaka a yankin na Darfur bayan barkewar rikicin, yayin da wasu sama da miliyan 2 da dubu 500 suka rasa muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.