Isa ga babban shafi
Mali

An rage adadin mutanen da mahara suka hallaka a Mali

Hukumomin kasar Mali sun rage adadin mutanen da suka ce an hallaka, a kisan gillar da ake zargin Fulani da aikatawa kan ‘yan kabilar Dogon daga mutane 95 zuwa 35.

Jami'an gwamnatin Mali da wasu 'yan kabilar Dogon a gaf da wasu sabbin kaburbura a kauyen Sobane-Kou.
Jami'an gwamnatin Mali da wasu 'yan kabilar Dogon a gaf da wasu sabbin kaburbura a kauyen Sobane-Kou. AFP
Talla

Sanarwar gwamnati tace cikin mutanen da aka kashe 24 yara ne kanana, yayin da tuni aka kama mutane 6 da ake zargin cewar suna da hannu wajen kai harin.

A ranar litinin da ta gabata, hukumomin tsaron Mali suka bayyana cewa, wasu mahara da ake zargin Fulani ne, sun kai harin ramuwa kan kauyen Sobane Kou da ke yankin tsakiyar kasar, inda suka hallaka yan kabilar dogon akalla 100.

Wannan harin na zuwa ne kasa da watanni uku bayan wasu mahara da ake zargi ‘yan kabilar Dogon suka halaka akalla mutane 160, Fulani a wani kauye.

Wannan kisa ya haifar da suka daga ciki da wajen kasar, harma da Majalisar Dinkin Duniya wadda ta bukaci gudanar da bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.