Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun sake kashe mutane da dama a Mali

Akalla mutane 100 ne aka kashe a wani mummunan hari da wasu mahara suka kai wani kauye a tsakiyar kasar Mali, a harin baya bayan nan da ya addabi yankin.

Taswirar da ke nuna kauyen Sobane-Kou a Mali inda 'yan bidiga suka halaka mutane 100.
Taswirar da ke nuna kauyen Sobane-Kou a Mali inda 'yan bidiga suka halaka mutane 100. AFP
Talla

Ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin wannan hari, amma kisan dimbim jama’ar da aka yi a garin na al’ummar Dogon ya yi kama da ramuwar gayya.

Wannan harin na zuwa ne kasa da watanni uku bayan wasu mahara da ake zargi ‘yan al’ummar Dogon ne da ba a san ko su waye ba, sun halaka akalla mutane 160,‘yan kabilar Fulani a wani kauye.

Jami’ai a gundumar Koundou, inda kauyen Sobane – Kou yake, sun ce an samu gawarwaki 95 a kone, kuma suna ci gaba da neman saura 19 da suka bace, haka kuma an yanke dabbobi da dama, sannan aka cinna wa gidaje wuta.

Kamfanin dillancin labaran Fransa ya ce ta ji wata majiyar tsaro a Malin na cewa an shafe ilahirin al’ummar wani kauyen Dogon daga doron kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.