Isa ga babban shafi
Afrika

Majalisar Sojin Sudan ba zata mika El Bashir ga kotun Duniya ba

Sojojin Sudan da suka kifar da gwamnatin shugaba Omar al-Bashir, sun bayyana cewa ko shaka ba za su mika El Beshir zuwa kotun Duniya ba,banda haka zasu kafa Gwamnatin rikon kwariya da farraren hula a yau juma’a ,sanarwa daga daya daga cikin manyan hafsan sojan kasar gaban manema labarai a Khartoum.

Masu zanga-zanga a kasar Sudan
Masu zanga-zanga a kasar Sudan AFP
Talla

Sojojijn ta bakin Ministantsaro ya sanar da cewa, sun kafa dokar ta-baci ta tsawon watanni uku, yayinda ya ce, kasar ta tsunduma cikin matsaloli da dama da suka hada da cin hanci da rashawa da rashin adalci har ma da rashin jagoranci na gari.

Ministan ya bayar da hakuri kan asarar rayukan da aka samu da kuma tashe-tashen hankulan da suka barke a yayin gudanar da zanga-zangar kin-jinin shugaba al-Bashir.

Tuni aka dakatar da aiki da kundin tsarin mulkin kasar, yayinda aka rufe kan iyakokin kasar har sai baba-ta-gani.

Kawar da gwamnatin al-Bashir da ya shafe shekaru 30 akan karagar mulki na zuwa ne bayan zanga-zangar adawa da gwamnatinsa da al’ummar kasar suka gudanar.

Ana sa ran sanarwar da sojojin suka yi za ta kwantar da hankulan jagororin kungiyoyi da suka banzama a wannan zanga-zanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.