An girke sojoji a babban birnin Sudan
Rundunar Sojin Sudan ta girke jami’anta a birnin Kahrtoum a daidai lokacin da masu zanga-zanga ke bukatar sojojin kasar da su tsoma baki kan tilasta wa shugaba Omar al-Bashir sauka daga mukaminsa.
Wallafawa ranar:
Rahotanni na cewa, wasu daga cikin sojojin sun nun alamar bai wa masu zanga-zangar kariya bayan wasu jami’an tsaro na daban sun harba hayaki mai sa kwalla kan masu zanga-zangar da suka yi zaman dirshen,
Shaidu sun ce, sojojin sun yi fatattaki wasu manyan motoci da ke cilla barkonon-tsohuwa kan masu zanaga-zagar.
Babu cikakken bayani kan jami’an tsaron da suka cilla barkonon-tsohuwar, amma bayanai na cewa, ma’aikata ne a Hukumar Leken Asirin Kasar.
Masu zanga-zangar na fatan sojojin za su yi wa shugaban kasar juyin mulki bayan ya shafe kusan shekaru 30 a kan karagar mulki.
Kawo yanzu, shugaba al-Bashir ya ki amincewa da bukatar kafa gwamnatin rikon kwarya duk da tsawon lokacin da aka shafe na gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatinsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu