Fayulu ya bukaci kotun koli ta soke zaben Jamhuriyar Congo
Martin Fayulu dan takarar ‘yan adawa da yazo na biyu a zaben shugabancin Jamhuriyar Congo, ya shigar da kara kotun kolin kasar, inda ya bukaci ta soke sakamakon zaben, saboda magudin da yake zargin an tafka.
Wallafawa ranar:
Fayulu wanda ke ikirarin shi ne ya lashe zaben da ya gudana a ranar 30 ga watan Disamba, ya zargi Wanda hukumar zaben kasar ta baiwa nasara Felix Tshisekedi da cimma yarjejeniyar sirri da shugaba mai ci Joseph Kabila wajen murde zaben.
Nasarar Tshisekedi a zaben kasar ta Jamhuriyar Congo dai ta gamu da turjiyar, sauran ‘yan adawa, tawagar masu sa’ido ta kasashen turai, da kuma majalisar shugabannin cocin katolika na kasar mai wakilai dubu 40,000, wadanda suka ce sakamakon zaben ba sahihi bane.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu