Isa ga babban shafi
Sudan-Zanga-Zanga

Jami'an tsaro sun kashe mutane 37 a zanga-zangar Sudan - Amnesty

Kungiyar Amnesty International ta yi ikirarin cewa akalla mutane 37 jami’an tsaron Sudan suka hallaka cikin daruruwan Jama’ar da ke zanga-zangar adawa da karin farashin Burodi da gwamnatin kasar ta yi.Ikirarin na Amnesty na zuwa a dai dai lokacin da gwamnatin ta sanar da Jibge tarin jami’an tsaro don dakile zanga-zangar mafi muni da masu gangamin suka shirya gudanarwa a gobe Laraba.

Yanzu haka dai zanga-zangar ta juye zuwa ta kyamar gwamnati matakin da ya tilasta girke tarin jami'an tsaro don dakile ta.
Yanzu haka dai zanga-zangar ta juye zuwa ta kyamar gwamnati matakin da ya tilasta girke tarin jami'an tsaro don dakile ta. Reuters
Talla

A cewar Amnesty International gwamnatin Sudan ta boye adadin da jami’an tsaron suka hallaka har lahira inda ko a shekaran jiya ta sanar da cewa mutane 8 kacal suka mutu yayinda ganau suka tabbatar da kirga gawar mutane 22 tun bayan fara zanga-zangar a Larabar makon jiya.

Amnesty International cikin bayanan da ta fitar yau din nan, ta ce tana da tabbacin mutane 37 da jami’an tsaron suka harbe har lahira daga cikin dubban da suka tsunduma zanga-zangar don nuna adawa da matakin gwamnati na karin farashin burodi zuwa ninki 3 wanda suka yi ittifakin wani mataki ne na kara tsadar rayuwa.

Har yanzu dai gwamnatin ta Sudan na ikirarin mutane 8 ne kadai suka mutu yayinda da ta kare jami’anta da cewa basu da laifi a rasa rayukan mutanen, domin kuwa suna kokarin tabbatar da tsaro ne.

Sai dai Amnesty International ta ce baya ga mutanen 37 da suka mutu cikin kasa da mako guda, akwai kuma tarin wadanda suka jikkata sakamakon yadda jami’an tsaron ke nuna karbi wajen dukansu da zarar sun hai manyan tituna don nuna fushinsu ga matakin na gwamnati.

Dubban jama'a a manyan biranen kasar ciki har da Khourtum sun tsunduma zanga-zangar ne don nuna adawa da karin farashin Burodin zuwa ninki 3, zanga-zangar da yanzu haka ta juye zuwa ta kyamar gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.