Isa ga babban shafi
Zimbabwe-Afrika ta Kudu

Afrika ta Kudu ta bada sammacin kama Mugabe

Masu shigar da kara na gwamnatin Afrika ta Kudu sun bada sammacin kama Uwargidan tsohon shugaban Zimbabwe, Grace Mugabe bisa zargin ta da lakada wa wata budurwa duka a shekarar 2017.

Uwargidan tsohon shugaban Zimbabwe, Grace Mugabe
Uwargidan tsohon shugaban Zimbabwe, Grace Mugabe REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Wannan na zuwa ne bayan kotu ta janye rigar kariyar Grace Mugabe a ickin watan Yulin da ya gabata.

Gabriella Engel ta zargi Mrs. Mugabe da yin amfani da wayar wutar lantarki wajen lakada mata duka a dakin wani otel da ke birnin Johannesburg.

Koda yake Uwargida Mugabe ta ce, ta yi mata dukan ne don kare kanta bayan budurwar ta kai mata hari da wuka a cikin maye .

Al’amarin ya faru ne watanni uku gabanin sojoji su karbe iko da tafiyar da mulkin Zimbabwe daga hannun Robert Mugabe wanda aka tilasta masa yin murabus bayan shafe tsawon shekaru 37 kan karagar mulki.

yanzu babu wani martani daga gwamnatin Zimbabwe ko kuma Mugabe dangane da sammacin, yayin da Kungiyar AfriForum ta yi madalla da sammacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.