Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Tsakiyar Afrika

shugaban Afrika ta Tsakkiya ya yaba da taimakon Rasha ga kasarsa

Shugaban jamhuriyar Afirka ta tsakiyar Faustin-Archange Touadera, ya yaba wa kasar Rasha sakamakon aikewa da dakarunta da kuma kayan aiki ga rundunar sojin kasar.Faustin-Archange, ya ce sakamakon yadda kasar ke fama da matsaloli masu nasaba da rashin tsaro, a shirye suke su yi hulda da duk wata kasa da za ta taimaka masu.

shugaban kasar Afrika ta tsakkiya  Faustin-Archange Touadéra la wani taron manema labarai a 11 afrilu 2018 a Bangui.
shugaban kasar Afrika ta tsakkiya Faustin-Archange Touadéra la wani taron manema labarai a 11 afrilu 2018 a Bangui. FLORENT VERGNES / AFP
Talla

Kasantuwar Rasha tare da mu, na nuni da yadda kasar ta amince ta ba mu makamai a matsayin gudunmuwa don karfafa jami’an tsaronmu, wadanda kowa ya sani cewa suna cikin yanayi na rashin kayan aiki.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta sha fama da matsaloli, wannan ne ma ya sa muke kira ga dukkanin kasashen duniya domin su zo su bayar da tasu gudunmuwa, akwai kalulabe da dama a gabanmu, saboda haka ba za mu rungume hannuwa ba a daidai lokacin da kasashe kamar Rasha suka amince su kawo mana dauki.

A dunkule, ina son sanar da ku cewa wannan tallafi ne da kasar Rasha ta ba mu, domin sake gina rundunonin tsaronmu domin ta haka ne kawai za a iya tabbatar da tsaro da kuma cigaba da kare hukumomin kasarmu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.