Isa ga babban shafi
Mali

"Ba zan amince da sakamakon zaben Mali ba"

Dan takaran zaben shugaban kasar Mali daga jam’iyyar adawa, Soumaila Cisse ya ce, ba zai amince da sakamakon zaben da aka gudanar a karshen mako ba saboda magudin da aka tafka da kuma tashin hankalin da aka samu.

Jagoran 'yan adawar Mali Soumaïla Cissé,
Jagoran 'yan adawar Mali Soumaïla Cissé, Twitter/ Soumaïla Cissé
Talla

Cisse ya bukaci magoya bayansa da su tashi tsaye domin kwatarwa kansu 'yanci, saboda ba za su amince da kama karya da kuma magudin zabe ba.

Gwamnatin Mali ta ce, kusan mazabu 500 ba su gudanar da zabe ba saboda fargabar tashin hankali daga 'yan bindiga kamar yadda Ministan Tsaro Salif Traore ya bayyana.

Har yanzu ana ci gaba da kidayar kuri’u, in da shugaba Ibrahim Boubacar Keita ke sahun gaba wajen samun ‘yawan kuri’un.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.