Isa ga babban shafi

'Yan majalisa sun baiwa kansu bashin dala 40,000

‘Yan majalisar dokokin Sudan ta Kudu sun bai wa kansu bashin dala dubu 40 domin sayen motocin hawa.

Wasu kananan yara da yaki ya tilastawa tserewa daga muhallansu a Sudan ta Kudu, yayi daukar karatu a ajin wucin gadi da ke wajen birnin Juba. 12 ga watan Yuli, 2018.
Wasu kananan yara da yaki ya tilastawa tserewa daga muhallansu a Sudan ta Kudu, yayi daukar karatu a ajin wucin gadi da ke wajen birnin Juba. 12 ga watan Yuli, 2018. REUTERS/Andreea Campeanu
Talla

Kowanne daga cikin ‘yan majalisar dai na daukar albashin dala 50 ne a wata, abin da ya sa ake diga ayar tambaya kan yadda za a yi, su iya biyan wannan bashi.

‘Yan majalisar Sudan ta Kudun na ci gaba da fuskantar kakkausar suka daga al’ummar kasar da kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam, kasancewar, matakin ya zo ne, a dai dai lokacin da dubban ‘yan kasar ke cikin bukatar samun agajin gaggawa dangane da samun abinci da magunguna.

A baya bayan na, majalisar dinkin duniya, ta wallafa wani rahoto da ya yi hasashen cewa, sama da ‘yan kasar Sudan ta Kudu, miliyan 7, fiye da rabin a’ummar kasar ne za su bukaci agajin abinci cikin shekarar 2018 da muke ciki.

Bayan shekaru biyu da samun ‘yancin kai daga Sudan a shekarar 2011, yakin basasa ya barke a Sudan ta Kudu, biyo bayan rikici bisa shugabancin kasar da ya barke tsakanin Shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.