Isa ga babban shafi
Afrika

Iyaye na musayar 'ya'yansu mata da shanu a Afrika

Matsalar sauyin yanayi da yake-yake da kuma bakin-talauci na tilasata wa iyaye bayar da ‘ya’yansu mata don karbar shanu ko awaki a madadinsu a kasashen da ke yankin gabashin Afrika.

Talauci na tilasta wa iyaye karbar shanu don mika 'ya'yansu mata  ga masu bukatar auren su a wasu kasashen gabashin Afrika
Talauci na tilasta wa iyaye karbar shanu don mika 'ya'yansu mata ga masu bukatar auren su a wasu kasashen gabashin Afrika Getty Images/Aldo Pavan
Talla

Kungiyar da ke yaki da yi wa ‘yan mata auren dole ta ce, nahiyar Afrika na da kasashe 9 daga cikin 10 da ake da su a duk fadin duniya da ke fama da matsalar auren dole ga ‘yan mata a bisa dalilai na alada ko takaicin daukan ciki gabanin halastaccen aure ko kuma bakin-talauci.

Sai dai a baya-bayan nan, masu fafutukar ‘yancin bil’adama sun ce, yake-yake da sauyin yanayi na kan gaba wajen haddasa matsalar auren dole ga kananan yara mata da shekarunsu bai wuce 18 ba, musamman a Sudan ta Kudu, in da matsalar ta kai kashi 52 daga kashi 40 a shekarar 2010 kamar yadda alkaluman Majalisar Dinkin Duniya suka nuna.

Dorcas Acen, jami’a a kungiyar CARE International a Sudan ta Kudu ta ce, a halin yanzu, da dama daga cikin iyaye na aurar da ‘ya’yansu saboda matsalar tattalin arziki da ta tsananta a dalilin yake-yake.

Acen ta ce, lamarin ya kai la haula, domin kuwa iyayen na karbar ladar shanu 300 a matsayin farashin aurar da ‘ya’yansu.

A can kasar Kenya ma dai haka lamarin yake, in da makiyaya ke musayar ‘ya’yansu mata don karbar awaki bayan wani ibtila’in fari da ya hallaka dabbobi da dama a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.