Isa ga babban shafi

Habasha da Eritrea sun soma yunkurin sulhunta rikicin iyaka

Fira ministan Habasha Abiy Ahmed, ya fara ziyara a Eritrea domin ganawa da takwaransa Isaias Afwerki a babban birnin kasar Asmara a kokarin maido da kyakkyawar dagantaka tsakaninsu.

Sabon Fira Ministan Habasha, Abiy Ahmed.
Sabon Fira Ministan Habasha, Abiy Ahmed. REUTERS/Tiksa Negeri/File Photo
Talla

Tattaunawar shugabannin za ta mayar da hankali ne wajen kawo karshen rikicin kan iyaka a garin Badme da ke tsakanin kasashen biyu, wanda har yanzu Habasha ba ta kai ga janye sojinta daga wajen ba.

A shekarar 19998 zuwa 2000 ne kazamin rikici ya barke tsakanin kasashen na Habasha da Eritrea dangane da kan iyaka, yakin da ya yi sanadin hallakar kimanin mutane dubu 80, 000 daga dukkanin bangarorin biyu.

Tun bayan zama sabon Fira Ministan Habasha a watan Afrilu na shekarar 2018, Abiy Ahmed ya sha alwashin kawo karshen wannan tsamin dagantaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.