Isa ga babban shafi

Harin bam a jikkata mutane 83 a Addis Ababa

Akalla mutane 83 sun jikkata a kasar Habasha, sakamakon wani harin gurneti da aka kai kan taron gangamin goyon bayan sabon Firaministan kasar Abiy Ahmed.

Jami'an tsaron kasar Habasha, yayinda suka ke kokarin killace inda akai kai harin bam a birnin Addis Ababa.
Jami'an tsaron kasar Habasha, yayinda suka ke kokarin killace inda akai kai harin bam a birnin Addis Ababa. Yona Tadese/AFP
Talla

Seyoum Teshome, wanda ya jagoranci shirya gangamin goyon bayan Firaministan kasar ta Habasha a Addis Ababa, ya ce wanda ya kai harin gurnetin, ya yi nufin samun shugaban ne domin hallaka shi, amma jami’an ‘yan sanda suka dakile yunkurin nasa.

A jawabin da ya gabatar jim kadan bayan killace shi daga fuskantar barazanar harin, fira minista Abiy Ahmed ya ce mutane kalilan ne suka hallaka, sai daai daga bisani mai magana da yawunsa Fitsum Arega ya ce babu wanda ya rasa ransa a harin, illa mutane 83 da suka jikkata.

Firaminista Abiy Ahmed dai ya bayyana harin a matsayin wanda aka shirya sosai kafin kai shi a filin wasa na Meskel Square, sai dai bai kai ga bayyana zargin kowa bisa kai harin ba.

Sai dai a gefe guda ana ci gaba da samun bayanai masu cin karo da juna, inda wasu kafafen yada labaran ke rawaito cewar yawan wadanda suka jikkata a harin bam din ya haura 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.