Isa ga babban shafi
Najeriya-Ta'addanci

Najeriya ta tsananta matakan tsaro saboda zargin shigowar ISIS

Hukumomin tsaro a Najeriya sun kara tsananta matakan tsaro a ilahirin filayen jirgin saman kasar cikin wannan wata bayan wasu rahotanni da ke zargin akwai wasu shiryayyun hare-hare da mayakan kungiyar ISIS na kasashen Iraqi da Syria ke shirin kaddamarwa a kasar.

Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja babban birnin Najeriya.
Filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja babban birnin Najeriya. guardian.ng
Talla

Hukumomin tsaron Najeriyar sun ce kawo yanzu babu wata shaida da suka samu da ke nuna yiwuwar kai hare-haren daga kungiyar ta ISIS, amma akwai fargabar shigowarsu kasar don hadewa da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram musamman bayan fattakarsu daga Iraqi Syria da ma sauran kasashe a gabas ta tsakiya

Wata sanarwa da Ofishin sakataren gwamnatin Najeriyar ya fitar ta bukaci hukumar da ke kula da sufurin jiragen sama ta kasar da hukumar da ke kula da filayen jiragen saman dama hukumar Kwastam mai yaki da fasakwauri sun tsananta matakan tsaro don ganin ISIS din bata samu sukunin shigowa Najeriyar ba.

Ko da dai kasashen Afrika basa cikin jerin kasashen da ke fuskantar kalubalen ISIS kai tsaye amma samun burbushin kungiyoyin da ke biyayya gareta a kasashen na Afrika na matsayin babbar barazana ga tsaron kasashen.

A Najeriya dai akwai tsagin kungiyar Boko Haram karkashin Abu Mus’ab Al-Barnawi da ke biyayya ga uwar kungiyar ta ISIS wadda ta bashi mukamin mai jagorancin kungiyar a bangaren Yammacin Afrika.

A bangare guda akwai sanarwar ranar 22 ga watan Aprilu da Abu Hassan Al-Muhajir mai magana da yawun kungiyar ta ISIS ya fitar da ke nuna cewa kungiyar na daukar matakan fadadawa tare da sauya ayyukanta a wasu kasashen duniya.

Kusan dai za a iya cewa ISIS ta sauya salon kai hare-haren zuwa kai hari da wuka kamar yadda ya ke faruwa a wasu daga cikin manyan kasashe.

Haka zalika kusan za a iya cewa daga cin salon da ta sauya akwai kai hare-hare kan jiragen sama kamar dai yadda ta yi ikirarin haddasa hadarin jirgin saman Rasha na shekarar 2015 wanda ya hallaka 224.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.