Isa ga babban shafi
Guinea Bissau

An aiwatar da zaman majalisa karon farko cikin shekaru a Guinea Bissau

Karo na farko a cikin shekaru biyu, a yau alhamis Majalisar dokokin Guinea Bissau na gudanar da zamanta, kwanaki biyu bayan da bangarorin siyasar kasar suka cimma jituwa kan nada sabon firaminista.

Shugaba José Mário Vaz kenan na Guinea Bissau wanda al'ummar kasar ke zargi da assasa rikicin siyasar tun bayan da ya kori Firaministan kasar Domingos Simoes daga bakin aiki.
Shugaba José Mário Vaz kenan na Guinea Bissau wanda al'ummar kasar ke zargi da assasa rikicin siyasar tun bayan da ya kori Firaministan kasar Domingos Simoes daga bakin aiki. © Sia Kambou, AFP
Talla

A ranar Talatar da ta gabata ne aka rantsar da sabon Firaministan kasar Guinea Bissau Aristide Gomes domin kawo karshen rikicin siyasar da ya mamaye kasar da ke Yankin Afirka ta Yamma.

Sabon Firaministan Aristide Gomes ya sha alwashin kawo karshen rikicin siyasar Guinea Bissau wadda ta dade ba tare da shugaban gwamnati ba, saboda rikicin siyasa.

Gomes ya ce samun nasarar aikin sa na daga shugaban kasa Jose Mario Vaz da kuma shugabannin siyasar kasar wadanda suka dade suna kokawar iko, matakin da ya hana kasar cigaba.

Tuni shugaba Vaz ya sanar da kungiyar ECOWAS nadin Gomes wanda ya taba raki mukamin Firaminista tsakanin shekarar 2005 zuwa 2007.

Daya daga cikin manyan kalubalen dake gaban Firaministan, shine gudanar da zaben Yan Majalisu a watan Nuwamba mai zuwa.

Guinea Bissau ta fada rikicin siyasa tun shekarar 2015 lokacin da shugaba Vaz ya kori Firaminista Domingos Simoes Pereira, matakin da ya sa kungiyar ECOWAS shiga tsakani domin kawo karshen rikicin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.