Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya za ta ci gaba da bankado wadanda suka wawure dukiyarta

Gwamnatin Najeriya ta sha alwashin cigaba da bayyana sunayen mutanen da ake zargi da sace dukiyar talakawa, bayan ta gabatar da irin wadannan sunaye sau biyu a baya.

Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari dai ya sha alwashin yakar matsalar cin hanci da rashawa da ta dabaibaye Najeriyar baya ga fatattakar masu wawure dukiyar al'umma da ma dawo da dimbin duniyar kasar da aka jibge a kasashen ketare.
Shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari dai ya sha alwashin yakar matsalar cin hanci da rashawa da ta dabaibaye Najeriyar baya ga fatattakar masu wawure dukiyar al'umma da ma dawo da dimbin duniyar kasar da aka jibge a kasashen ketare. REUTERS/Dan Kitwood
Talla

Ministan yada labaran Najeriyar Lai Muhammed wanda ya bayyana haka a Lagos, ya ce tun bayan bayyana sunayen da akayi na farko, wasu mutane na ta yi wa gwamnatin jan ido da barazana, cikin su har da kafofin yada labarai.

Lai Muhammed ya ce ya san gwamnati bata da hurumin kotu na hukunta wadanda ake zargi, amma kuma suna da hurumin shaidawa Yan Najeriya wadanda su ka sace dukiyar su.

Akasarin sunayen da aka gabatar wa Yan Najeriya na wadanda suka sace dukiyar talakawan sun fito ne daga jami’an tsohuwar gwamnatin da ta gabata, abinda ya sa wasu ke barazanar zuwa kotu domin wanke sunan su akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.