Isa ga babban shafi
Botswana

Shugaban Botswana Ian Khama ya sauka daga mukaminnsa

Shugaban Kasar Botswana Ian Khama ya sauka daga mukamin sa bayan kwashe shekaru 10 a karagar mulki, inda ya mika ragamar tafiyar da kasar ga mataimakin sa Mokgweetsi Masisi.

Ian Khama Tsohon Shugaban kasar Botswana
Ian Khama Tsohon Shugaban kasar Botswana Reuters
Talla

Masisi ne ya zama shugaban kasa na uku da zai jagoranci kasar daga Jam’iyyar Khama wadda ta mamaye harkokin siyasar kasar.

Sabon shugaban mai shekaru 55 ya taba aiki da Majalisar Dinkin Duniya kafin ya zama dan majalisa a shekarar 2009.

Tsakanin shekarar 2011 ya rike mukamin ministan harkokin jama’a da kuma ministan ilimi, kafin nada shi mataimakin shugaban kasa bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.