Isa ga babban shafi
AU-NAJERIYA

Dalilin Najeriya na kin amincewa da yarjejeniyar kasuwancin Afirka

Shugabannin kasashen Afirka sun rattaba hanu kan yarjejeniyar kasuwancin bai-daya da aiwatar da ita zai sa ciniki tsakanin kasashen zai kai kudin da yawasu ya zarta dataa triliyan uku, a wani biki da aka yi a Kigali kasar Rwanda.

Zauren taron da aka kulla yarjejeniyar cinikayyar bai-daya tsakanin kasashen Afrika da ke birnin Kigalaili na Rwanda
Zauren taron da aka kulla yarjejeniyar cinikayyar bai-daya tsakanin kasashen Afrika da ke birnin Kigalaili na Rwanda © REUTERS/Jean Bizimana
Talla

Akalla mutane biliyan daya da miliyan 200 ne za su  amfana da wannan yarjejeniya matukar aka fara aiwatar da ita.

Kasashe ne 44 suka sanya hannu kan shirin da ake bukatar kasashe 22 domin fara shi, yayin da Najeriya da Afirka ta Kudu, kasashen da suka fi karfin tattalin arziki suka kauracewa bikin.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa da masu masana’antua Najeriya Frank Jacobs, ya bayyana gamsuwarsu dangane da matakin da Najeriya ta dauka na kin sanya hannu kan yarjejeniyar.

Jacob ya ce ‘’Kungiyar kasashen Turai da kasar Moroko na da yarjejeniyar kasuwanci a tsakaninsu, kuma wannan yarjejeniya ta bai wa Turai damar shigar da kayayyakinta zuwa Moroko, da zarar wadannan kayayyaki sun isa Moroko, to ana iya canja musu hatimin da ke jiki, a ce a Moroko ne aka sarrafa su, hakazalika Maroko za ta iya shigo da su Najeriya karkashin yarjejeniyar da aka kulla a Kigali’’.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwar na Najeriya ya ci gaba da cewa, ‘’wannan shi ne dallilin da ya sa muka ki amincewa har sai an warware matsalar  sannan an tabbatar mana hanyar da za’a bi wajen samar da kuduri da zai warware wannan batu’’.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.