Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisun Najeriya sun amince da sauyi ga zabukan kasar

Zauren Majalisun Dattawa da na Wakilan Najeriya sun amince da sauya tsarin manyan zabukan kasar, sabanin yadda aka saba gudanarwa a baya, kamar yadda hukumar zaben kasar mai zaman kanta INEC ta tsara gudanarwa a shekarar 2019.

Shugaban Majalisar dattijan Najeriya Sanata Abubakar Bukola Saraki.
Shugaban Majalisar dattijan Najeriya Sanata Abubakar Bukola Saraki. NAN
Talla

A baya dai bisa al'ada a tsarin zaben Najeriyar akan fara gudanar da zaben shugaban kasar ne, kana na ‘yan majalisun tarayya ya biye masa baya sai kuma na gwamnoni da 'yan majalisun jihohi daga karshe.

Sai dai karkashin sabon tsarin da hukumar ta INEC ta gabatarwa Majalisar yayin zaben na 2019 za a fara gudanar da zaben ‘yan majalisun tarayya ne, kafin daga bisani a gudanar da na Gwamnoni, sannan na shugaban kasa ya biyo baya.

Ko da ya ke dai rahotanni sun ce, Shugaban Majalisar Dattijan Najeriyar Abubakar Bukola Saraki bai bayar da cikakkiyar dama ga sauran mambobin majalisar don tafka muhawara kan batun ba, lamarin da ya tilasta musu kiran taron manema labarai don nuna cewa ba da hannunsu majalisun suka amince da batun ba.

A bangare guda dai, zauren Majalisun biyu sun jaddada cewa da kyakkyawan nufi suka amince da sabon tsarin na INEC, kuma koda sashin zartarwa yaki sa hannu kan dokar, za su yi amfani da damar da kundin tsarin mulki ya basu wajen zartars da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.