Isa ga babban shafi
Masar

Sojin Masar sun kaddamar da sabon farmaki kan 'yan ta'adda

Rundunar sojin Masar ta kaddamar da farmaki a sassann kasar, kan kungiyoyin ‘yan ta’adda da kuma sauran gungun masu aikata laifuka.

Wasu jami'an tsaron kasar Masar yayin da suke sintiri a yankin Sinai domin murkushe barazanar kungiyoyin 'yan ta'adda.
Wasu jami'an tsaron kasar Masar yayin da suke sintiri a yankin Sinai domin murkushe barazanar kungiyoyin 'yan ta'adda. AFP
Talla

Kakakin sojin na Masar Kanal Tamer Rifai ya ce sun kaddamar da farmakin ne a Yankin Sinai, da kuma yankunan kasar da suke yamma da Hamada, domin murkushe kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Tuni dai rundunar sojin Masar ta kara matakan tsaro a asibitocin da ke kasar da kuma shirya daukar matakan bada agajin gaggawa da samar da magunguna. Zalika rundunar sojin ta kara matakan tsaro a ilahirin tashoshin jiragen ruwa na kasar.

Masar ta shafe shekaru tana yaki da mayakan sa kai da ke yi wa gwamnatin bore, musamman a yankin Sinai da hare-hare kan jami’an tsaron kasar ke dada karuwa a baya bayan nan.

Akalla mutane 235 suka hallaka a wani harin bam da aka kai kan wani Masallaci a arewacin yankin Sinai, a lokacin da mutanen suke tsaka da gabatar da Sallah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.