Harin kunar bakin wake ya hallaka sojin Masar sama da 20
Wani harin kunar bakin wake da aka kai kan shingen bincike soji, a arewacin Sinai da ke Masar, ya hallaka akalla jami’an sojin kasar 26.
Wallafawa ranar:
Dan kunar bakin waken yayi amfani da mota, makare da bama-bamai, inda ya danna kai zuwa shingen binciken jami’an sojin a kudancin kauyen Rafah, ya gabza ta, nan take kuma ‘yan bindiga masu yawan gaske suka bude wuta, inda suka raunata sojoji 26 bayan wasu 26 da suka hallaka.
Yayinda take tabbatar da aukuwar harin, rundunar sojin kasar, ta kuma ce jami’anta, sun yi nasarar hallaka mayaka Arba’in daga cikin maharan da suka far musu, wadanda ake zargin ‘yan kungiyar ISIS ne.
Tuni dai kungiyar ISIS da dauki alhakin kai harin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu