Isa ga babban shafi
Najeriya

Hare-haren 'yan bindiga na gab da zama tarihi a Najeriya - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya alkawarta cewa, hare-haren 'yan bindiga da ake danganawa da Makiyaya na dab da zama tarihi a ilahirin sassan kasar, la'akari matakan tsaro na fili da na boye da gwamnatin ta saka don kare rayukan al'ummar kasar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Ofishinsa da ke fadarsa ta Villa a Abuja babban birnin kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a Ofishinsa da ke fadarsa ta Villa a Abuja babban birnin kasar. Sunday AGHAEZE / NIGERIA STATE HOUSE / AFP
Talla

Muhammadu Buhari wanda ke cin wannan alwashi ta cikin wata sanarwa da Mai bashi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Mr Femi Adesina ya fitar yau Litinin, ya ce gwamnatin ta girke tarin jami'an tsaro a dukkanin yankunan da ake samun hare-haren.

Sanarwar ta ce Gwamnati na sane da halin matsi da kuma tsoro da al'ummar Najeriyar suka shiga sanadiyyar hare-haren wanda a baya-bayan nan ke kara ta'azzara tare da haddasa asarar rayuka, kuma babu shakka ta dauki kwararan matakai don magance matsalar.

A cewar Muhammadu Buhari ta cikin sanarwar, yana nan kan kudurinsa na ganin bai saba alkawura uku da ya daukarwa 'yan Najeriyar yayin yakin neman zabensa ba, wadanda suka kunshi samar da tsaro ta hanyar tsare rayuka da dukiyoyin al'umma, da habaka tattalin arziki ta hanyar yaki da cin hanci da rashawa da kuma baza komar tattalin arziki sai kuma samar da ayyukan yi ga al'umma.

Haka zalika sanarwar ta ce, gwamnatin na kuma iyakar kokarinta wajen ganin ta daidaita bangaren lantarki baya ga gyara tituna da kuma inganta walwala da jin dadin jama'a. 

Ko a yammacin jiya ma sai da wasu 'yan bindiga suka hallaka akalla mutane biyar a wani kauye da ke karamar hukumar Numan a Adamawa da ke yankin arewa maso gabashin kasar.

Kazalika hare-haren na kara ta'azzara a Najeriya yayinda a wasu yankunan ke kokarin juyewa zuwa rikicin kabilanci musamman tsakanin Fulani da sauran Kabilun kasar.

Ko da yake dai a lokuta da dama Shugabancin Fulanin na musanta batun hannu a hare-haren yayinda su ke zargin wasu da yin shigarsu tare da kai hare-haren don bata musu suna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.