Isa ga babban shafi
Masar

Sojojin Masar sun kaddamar da farmaki kan 'yan ta'adda

Rundunar sojin kasar Masar ta kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’adda a yankin Sinai, bayan mummunan harin da suka kai kan wani Masallacin Juma’a, inda suka hallaka mutane akalla 300.

Wasu daga cikin mutanen da harin ta'addancin da aka kai kan Masallacin Juma'a a Sinai ya ritsa da su, yayin da ake kokarin garzayawa da su asibiti.
Wasu daga cikin mutanen da harin ta'addancin da aka kai kan Masallacin Juma'a a Sinai ya ritsa da su, yayin da ake kokarin garzayawa da su asibiti. AFP
Talla

Sojin sun kaddamar da farmakin ne, bayan da shugaban kasar ta Masar, Abdul Fattah al-Sisi ya sha alwashin mai da martani mai zafin gaske kan ‘yan ta’addan.

Tuni dai rundunar sojin saman kasar, ta ce ta samu nasarar lalata wani rumbun ajiyar makmai da mafi akasarin motocin da ‘yan ta’addan suka yi mafani da su wajen kai harin ta’addancin kan Masallacin Juma’ar na Rawdah da ke arewacin yankin na Sinai.

Kafofin yadda labaran kasar sun ce maharan sun fara tada bam ne a masallacin, kafin daga bisani su bude wuta kan masu ibadar.

Shaidun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sun yi wa Masallacin kawanya da motoci bayan dasa bama-baman, domin datse hanyoyin fita daga cikin Masallacin.

Akalla mutane 109 ne suka jikkata a harin, wanda har yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai wa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.