Isa ga babban shafi
Najeriya

Ina hakkokin masu taimaka wa EFCC da bayanai?

A Najeriya, sama da watanni shida bayan da wasu suka tseguntawa hukumar EFCC da bayanai don gano bilyoyin kudaden da aka boye a wani gida da ke unguwar Ikoyi a birnin Lagos, har yanzu gwamnati ba ta bai wa wadanda suka taimaka da bayanai domin gano kudaden hakkokinsu na 5% da doka ta ce a ba su ba, lamarin da zai iya sanyayya guiwar wadanda ke da niyyar taimakawa da irin wadannan bayanai.

Mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu
Mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu
Talla

Lauyan da ke kare wadannan mutane Barista Yakubu Galadima, ya ce ya kamata gwamnati ta tuna da cewa mutanen sun sadaukar da rayukansu ne domin kwato dukiyar Najeriya, inda suka yi sanya hannu kan yarjejeniyar da ke bayar da izinin tuhumarsu a gaban kotu matukar dai ba a gano komai a gidan da aka ce an boye kudaden ba.

Barista Galadima ya ce sun sha rubutawa hukumar ta EFCC da kuma fadar shugaban kasa wasiku don nema wa wadannan mutane hakkokinsu, amma har yanzu shiru. Duk yunkurin da muka yi domin jin ta bakin hukumar ta EFCC dangane da wannan batu ya ci tura.

Kimanin watanni 6 da suka gabata ne jami’an hukumar ta EFCC suka kai samame a wani gida da ke unguwar Ikoyo a birnin Lagos, tare da gano kudaden da suka hada da Naira, Dalar Amurka da kuma Fan na Ingila da aka kiyasta cewa sun kai haura Naira bilyan 17.

Daga bisani kotu ta bayar da umurnin mayar da kudaden a baitul mali saboda ba wanda ya yi ikirarin cewa mallakinsa ne, yayin mutane uku da suka taimaka wa hukumar yaki da rashawan da mabayai domin gano kudaden ke ci gaba da jira a ba su kason da doka ta ce a bai wa wanda ya tsegunta da bayanai domin karfafa wa jama’a guiwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.