Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Grace Mugabe ta gargadi juyin mulki a Zimbabwe

Uwargidan shugaban kasar Zimbabwe, Grace Mugabe ta gargadi yiwuwar kulle-kullen juyin mulki a dai dai lokacin da fafutukar neman maye gurbin mai-gidanta ta zafafa.

Grace Mugabe, uwargidan shugaban Zimbabwe Robert Mugabe na neman kujerar shugabancin kasar
Grace Mugabe, uwargidan shugaban Zimbabwe Robert Mugabe na neman kujerar shugabancin kasar REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Uwargidan ta ce, makusantan mataimakin shugaban kasa, Emmerson Mnangagwa na barazana ga rayuwar mutanen da su ka ki ba shi goyon bayan maye gurbin Robert Mugabe mai shekaru 93.

Grace Mugabe da Mnangawa na kan gaba wajen neman kujerar shugabancin kasar, yayin da hamayyarsu ta haddasa rabuwar kawuna a jam’iyyar Zanu-PF mai mulkin kasar.

Hamayyar ta dada zafafa ne bayan Mr. Mnangagwa ya zargi cewa, an sanya ma sa guba a cikin watan Agustan da ya gabata.

Magoya bayansa sun zargi masu adawa da shi ne a jam’iyyar Zanu-PF suka yi kokarin hallaka shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.