Isa ga babban shafi
Libya-Amurka

Gabashin Libya ta haramtawa Amurkawa zuwa kasar

Gwamnatin da ke iko da Gabashin Libya ta haramtawa Amurkawa zuwa kasar a wani matakin na mayar da martani kan umurnin shugaba Donald Trump na hana ‘yan Libya zuwa Amurka.

Gwamnatin da ke iko da Gabashin Libya ta haramtawa Amurkawa zuwa kasar
Gwamnatin da ke iko da Gabashin Libya ta haramtawa Amurkawa zuwa kasar REUTERS/Esam Omran Al-Fetori
Talla

Gwamnatin da ke karkashin Abdullah al-Thinni tare da kwamandan soji Khalifa Haftar ta bayyana cewar abin takaici ne yadda Amurka ta sanya sunan Libya cikin jerin kasashen da ta hana mutanen su zuwa Amurka.

Al-Thinni ya ce matakin Amurka bai dace ba la'akari da yadda sojojin kasar suka tashi tsaye suna yaki da ayyukan ta’addanci.

Libya na daga cikin kasashe 8 da Amurka ta bayyana a matsayin wadanda aka haramtawa jama’ar su zuwa Amurkan saboda tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.