Isa ga babban shafi
Nijar

'Yan kasuwar Nijar sama da 50 sun bace a hatsarin kwale-kwale

Wasu ‘yan kasuwa sama da 50 daga Jamhuriyar Nijar sun bace bayan kwale-kwalen da ke dauke da su ya kife a kogin River Niger da ke Najeriya.

Ana ci gaba da aikin neman 'yan kasuwar Nijar 53 da suka bace a hatsarin kwale-kwale a kogin River Niger da ke Najeriya
Ana ci gaba da aikin neman 'yan kasuwar Nijar 53 da suka bace a hatsarin kwale-kwale a kogin River Niger da ke Najeriya Getty Images/Shanna Baker
Talla

‘Yan kasuwar da suka fito daga yankin Gaya na Nijar, na kan hanyarsu ce ta zuwa cin kasuwa a karamar hukumar Bagudo da ke jihar Kebbi ta Najeriya.

Kimanin mutane 100 ne a cikin kwale-kwalen, in da aka yi nasarar ceto 47, yayin da 53 suka bace.

Shugaban karamar hukumar Bagudo, Alhaji Muhammad Kaura Zagga, ya shaida wa manema labarai cewa, hukumomin Nijar sun aiko da gwanayen iya ruwa har guda 500 don lalubo mutanen da suka bace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.