Somalia
Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Mutane 6 a Somalia
A kasar Somalia mutane akalla 6 suka gamu da ajalinsu sakamakon wani harin kunar bakin wake a wani gidan cin abinci na manya dake garin Beledweyne.
Wallafawa ranar:
Talla
Wani jami'in 'Yan Sanda Hussein Osman ya shaidawa kamfanin Dillancin labaran Reuters cewa mutane da yawa ne suka jikkata.
Wannan yanki na kusa ne da ofishin Gwanman gunduman Hiran, kuma an kai harin ne daidai wani lokaci da Gwamnan ke ganawa da wasu mutane.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu