Mutane 312 sun mutu a ambaliyar Saliyo
Akalla mutane 312 ne suka rasa rayukansu, in da sama da dubu 2 suka rasa gidajensu sakamakon ibtila’in ambaliyar ruwa a babban birnin Freetown na Saliyo a yau Litinin.
Wallafawa ranar:
Rahotanni na cewa, dakunan ajiye gawarwaki sun cika makil, kuma jama’a na ci gaba da neman ‘yan uwansu da makusantansu.
Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya ce, ya shaida yadda aka yi ta kwashe gawarwakin mutane da kuma yadda gidaje suka nutse a ruwa musamman a wasu yankuna biyu na birnin, in da ruwa ya mamaye manyan hanyoyi da unguwanni.
Kungiyar bada agaji ta Red Cross ta bayyana cewa, akwai yiwuwar alkaluman mamatan su karu nan gaba.
Wasu hotuna da aka yada sun nuna yadda aka dora gawarwaki kan juna.
Ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar mutuwar mutane 10 tare da raba dubbai da muhallansu a birnin Freetown a shekarar 2015.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu