Isa ga babban shafi
Nijar

Mutane sun kashe Dorinar ruwa 27 a Nijar

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun ce wasu mazauna kauyuka sun hallaka Dorinar ruwa 27 saboda zargin cewar suna lalata musu gonakki da kuma cinye musu kaji.

An girke Jami'an tsaro a yankin Ayorou domin hana kisan Dorina a Nijar
An girke Jami'an tsaro a yankin Ayorou domin hana kisan Dorina a Nijar rfi/Elisa Drago
Talla

Jando Rhichi Algaher, jami’in kula da yankin ya ce a watan Maris aka fara kai wa dorinar hari, daga bisani kuma abin ya kazance.

Ministan kula da muhalli Almoustapha Garba ya tabbatar da aukuwar lamarin da y ace ya faru a yankin Ayorou.

Kauyen Ayorou da ke da nisan kilomita 200 daga birnin Yammai na dauke da tarin dorinar ruwa da tsuntsaye, abinda ya mayar da yankin wajen yawon bude ido.

Ministan ya ce gwamnati ta yi alkawalin biyan diyya ga manoman da dabbar ta yi wa barna tare da yin kira ga mazauna yankin sun gujewa saba doka.

Akwai mutane 10 da aka cafke da ake zargi da kisan dorinar amma daga baya an sake su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.