Isa ga babban shafi
Philippines

Dorinar ruwa mafi tsufa a duniya ta mutu a Philippine

Dorinar ruwa da ake kira Bertha wacce aka bayyana mafi tsufa a duniya ta mutu tana da shekaru 65 a duniya a wani gandun dawa da ke garin Manila na kasar Philippine.

Dorinar ta shigo gandun dajin na Manila tun tana ‘yar shekaru 7 a shekarar 1959.
Dorinar ta shigo gandun dajin na Manila tun tana ‘yar shekaru 7 a shekarar 1959. gmanetwork
Talla

Bayanai sun ce Dorinar ta yi yawancin rai fiye da sauran nau'in dabbobin da ke cin ciyayi da ganyayyaki.

A ranar Juma’a ne aka iske Dorinar ta mutu mai nauyin ton 2.5. Kuma binciken da aka gudanar ya nuna cewa ta mutu ne bayan wasu sassan jikinta sun daina aiki.

Jami’an da ke kula da gandun dajin sun ce tun a 1980 namijin Dorinarta ya mutu ba tare da sun bar iri ba.

Dorinar ta shigo gandun dajin na Manila tun tana ‘yar shekaru 7 a shekarar 1959.

Yanzu wata Giwa ce da ake kira Mali ta rage a gandun dajin na Manila a matsayin mafi tsufa inda ta ke da shekaru 43 bayan mutuwar Bertha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.