Ambaliyar ruwa ta yi barna a Kaita Jihar Katsina
Akalla mutane 2,000 sun rasa matsuguninsu a karamar hukumar Kaita da ke Jihar Katsina a Najeriya, sakamakon ambaliyar ruwar da aka samu da ta rusa gidaje sama da 150.
Wallafawa ranar:
Hajiya Umma Abdullahi Mahuta, kantomar karamar hukumar Kaita ta shaidawa RFI Hausa cewa ambaliyar ta janyo hasarar dukiyoya ta miliyoyin kudi.
Hajiya Umma ta ce ambaliyar ta fi barna a Unguwar Wakilin Kudu inda gidaje 69 suka rushe da kuma unguwar Wakilin arewa da yamma da sabuwar Unguwa duk a cikin garin na Kaita inda gidaje da shaguna da dama suka rushe.
Sai dai Hajiya ta ce ambaliyar ba ta janyo hasarar rai ba.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Mukaddashin shugaban kasar Yemi Osibanjo ya bada umurnin sakin naira miliyan sama da dubu ga wasu Jihohin kasar domin taimakawa wadanda ambaliyar ta shafa.
A cikin makon nan gwamnatin Tarayyar ta yi gargadin cewa za a samu ambaliyar ruwa a jihohi 30 da kuma kananan hukumomi 100 da ke sassan kasar, sakamakon ruwan sama da ake tafkawa a daminar bana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu