Isa ga babban shafi
Najeriya

INEC ta sanar da Dino Melaye halin da ya ke ciki

Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce tabbas ta samu sa-hannun dubban mutane da suke nemi bukatar tube Dino Melaye dan Majalisar dattawa da ke wakiltar jihar Kogi.

Sanata Dino Melaye da ke wakiltar Kogi ta yamma
Sanata Dino Melaye da ke wakiltar Kogi ta yamma facebook
Talla

Hukumar zaben ta ce mutane dubu 188 da suka cancanci kada kuri’a daga mazabar Kogi ta yamma da Melaye ke wakilta suka sanya hannu kan bukatar.

A wata sanarwa da ta fitar, hukumar  INEC ta ce tuni ta sanar da Melaye cewa ta samu takardun kiranyen a wata wasikar ta da aike masa.

Dino Melaye dai na zargin gwamnan jihar Kogi Yahya Bello a matsayin wanda ke daukar nauyin yunkurin,  wanda ya ce ba zai yi nasara ba.

Ana dai takun saka ne tsakanin Dan majalisar dattijan da gwamnan Kogi duk da cewa suna jam’iyya guda ta APC.

INEC ta ce a ranar 3 ga watan Yuli za ta wallafa bayanai akan mutanen da suka sanya hannu kan bukatar kiranyen akan Melaye domin tabbatar da matsayinsu a mazabar dan majalisar dattijan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.