Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar ta janye jekadanta a Qatar

Nijar ta sanar da janye jakadanta daga Qatar domin nuna goyon baya ga Saudiya da kawanyenta da ke rikicin diflomasiyyar tsakaninsu da Qatar da suke zargi tana taimakawa ayyukan ta’addanci.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou today.ng/news/africa
Talla

Nijar ta bi sahun sauran kasashen Afirka ne da suka dauki irin wannan mataki, da suka hada Mauritania da Chadi da Senegal da kuma Gabon da ta yi kira ga Qatar da ta guji taimaka wa ‘yan ta’adda.
Tsohon Jekadan Nijar a Libya Issifou Bachard, ya danganta matakin da gwamnatin kasar ta dauka a matsayin kuskure.

"An tilastawa Nijar ne kuma babu wata riba da kasar za ta samu", a cewar Ambasada Bachard.

Manyan kasashen na Larabawa sun zargi Qatar da taimakawa kungiyoyin ta’adda da suka hada da al Qaeda da kungiyar IS da ke da’awar Jihadi a Syria da Iraqi.

A makwannin da suka gabata ne kafofin yada labaran Amurka suka wallafa wani rahoto da ke zargin Qatar da daukar nauyin ta’addanci.

Qatar ta musanta zargin tare da kaddamar da bincike akan kutsen da ta ce an yi wa kamfanin dillacin labaranta inda aka buga labari game da alakarta da Iran da kuma hasashen cewa Trump ba zai jima ba a matsayin shugaban Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.