Isa ga babban shafi
Kenya

Mutane 8 za su fafata a zaben shugabancin Kenya

Hukumar zaben Kenya ta amince da sunayen mutane 8 da za su tsaya takarar shugabancin kasar a zaben da za a yi a ranar 8 ga watan Agusta mai zuwa, ciki har da shugaba mai-ci Uhuru Kenyatta da baban abokin hamayarsa Raila Odinga.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta na cikin wadanda za su fafata a zaben shugabancin kasar a cikin watan Agusta
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta na cikin wadanda za su fafata a zaben shugabancin kasar a cikin watan Agusta ASHRAF SHAZLY / AFP
Talla

Tantance wadanda suka cancanci tsayawa takarar ya kawo karshen burin mutane da dama da suka nuna sha'awar shiga takarar, ciki har da wani mutum da aka ce ya yi kokarin durowa daga hawa na 6 na ginin hukumar zaben kasar bayan ya rasa tikitin tsayawa takarar.

Bayan shugaba Uhuru Kenyatta da abokin hamayarsa Odinga, da suka fafata tare a shekarar 2013, akwai ‘yan takara 3 daga kananan jam’iyyun adawa da wasu uku  daban daga jam’iyyu masu cin gashin kansu.

Odinga mai shekaru 72, ya yi kokarin gudanar da gangamin samun hadin kai daga shugabanni manyan ‘yan adawa, wanda ya sake haskaka tauraronsa bayan gaza samun nasara a shekarar 1997 da 2007 da kuma 2013.

Zaben na Agusta na tattare da manyan kalubale, kana akwai wasu mutane sama da dubu 10 da ke takarar mukaman ‘yan Majalisa da gwamnoni da kuma Majalisun Larduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.