Isa ga babban shafi
Kenya

An tsare ‘yan majalisu 7 a Kenya

A Kenya ana ci gaba da tsare wasu ‘Yan majalisa tare da wasu manyan ‘yan siyasa wadanda ake zargi da furta kalaman tunzura jama’a a yayin da kasar ke fuskantar rikicin siyasa kafin zaben shugaban kasa.

Shugaban kasar kénya Uhuru Kenyatta
Shugaban kasar kénya Uhuru Kenyatta TONY KARUMBA / AFP
Talla

Babbar kotun a Nairobi ta bayar da umurnin ci gaba da tsare ‘yan siyasar ne na tsawon kwanaki hudu har sai an kammala bincike kan zaergin da ake yi masu na furta wasu kalaman kiyayya da tunzura jama’a.

'Yan siyasar da ake tsare da su sun hada da ‘Yan majalaisar dokoki guda uku daga bangaren jam’iyya mai mulki da kuma senatoci hudu daga bangaren jam’iyyar adawa.

Dukkanin ‘yan majalisar sun kwana jiya a tsare, kuma za a ci gaba da tsare su har zuwa 17 ga wata.

Cafke 'yan siyasar kuma na zuwa ne bayan shafe makwanni 'yan adawa na zanga-zangar adawa da hukumar zaben kasar ta Kenya wacce madugun adawa Raila Odinga ke zargi ta yi murdiya a zaben 2013.

Ana dai zargin 'yan majalisar a bangaren jam’iyya mai mulki kuma na hannun damar shugaba Uhuru Kenyatta da yin barazanar halaka raila Odinga.

Sentocin da aka kame kuma a bangaren adawa ana zarginsu ne da abkawa shalkwatar 'yan sanda, tare da yin hasashen barkewwar rikici a kasar sakamakon gazarar shugaba Kenyatta na hada kan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.