Isa ga babban shafi
Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta musanta zargin yunkurin juyin mulki

Rundunar Sojin Najeriya ta musanta rade-radin yunkurin juyin mulkin da wasu ke cewa an yi a kasar, inda ta ce sam sojojin kasar ba su da niyar yi wa mulkin Dimokaradiya karan tsaye.

Kakakin rundunar Sojan Najeriya Birgediya Janar Usman Kukasheka
Kakakin rundunar Sojan Najeriya Birgediya Janar Usman Kukasheka via twitter
Talla

A wani taron manema labarai, Kakakin rundunar sojin kasar Burgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya ce dakarun kasar, masu biyayya ne ga dokokin Najeriya wadanda suka shimfida mulkin dimokaradiya.

"Sojoji Najeriya sun ta’allaka ne ga yin biyayya ga shugaban kasa kuma kwamandan sojoji da tsarin mulkin kasa", a cewar Janar Kukasheka.

Rundunar Sojin ta bukaci ‘Yan Najeriya su kwantar da hankalinsu domin babu batun karbar mulki ta hanyar karfi.

Sai dai Janar Kukasheka ya ce ana gudanar da bincike kan yadda wasu rahotanni suka ce ana zawarcin wasu sojoji domin juyin mulkin. A cewarsa hakki ne na kwamandoji su tsawatar tare da jan kunne.

Wannan na zuwa a yayin da fadar shugaban kasa ta bukaci ‘yan Najeriya su yi amfani da abin da rundunar sojin kasar ta bayyana kan yunkurin juyin mulkin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.