Taron shugabanin kasashen Musulmai da Amurka
Sarki Salman na Saudi Arabia ya bayyana fata mai kyau wajen taron da za’ayi tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da shugabanin kasashen Musulmai a karshen wannan mako wanda ya ce zai taimaka wajen bunkasa dangantaka da kuma mutunta juna.
Wallafawa ranar:
Taron wanda zai zama irin sa na farko a ziyarar wata kasa da Trump zai kai bayan hawa karagar mulki zata kumshi shugabanin kasashen dake tekun Fasha 6 da kuma wasu shugabanin kasashen Musulmi 18 da aka gayyata da suka hada da Turkiya da Azerbaijan da Jamhuriyar Nijar da kuma Indonesia.
Kasar Iran bata cikin kasashen da aka gayyata taron.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu